Sojojin Yamen Sun Lalata Hasumiyar Aramco A Hari Da Suka Kai

dakarun sojin kasar yamen sun kai hari a kasar saudiya na mayar da martani kuma sun rusa hasumiyar aramco

Dakarun sojin kasar yamen sun bada labarin cewa sun kai hare hare na ramuwar gayya kan kasar saudiya a yau lahadi inda suka lalata hasumiyar Aramaco sakamakon hare hare da kasar saudiya ke ci gaba da kai wa a kasar yamen

kamfanin dillacin labarai na AFP ya bada rahoton cewa shedun gani da ido  sun ce an kai hari kan cibiyar hada hadar kudi ta sarki Abdallah dake birnin riyad a kasar saudiya, da kuma babbar hasumiyar kamfanin mai na Aramco , wasu shaidu guda biyu kuma sun bada rahoton cewa an lalata wani gida da ake gudanar da ayyukan makamashi a ciki

sai dai dakarun sojin kasar saudiya sun sanar da kakkabo makamai masu linzami guda biyu da kasar yamen ta harba musu, wasu sun ce an samu asarar ne bayan da makaman suka tarwatse a lokacin kakkabosu

idan ana iya tunawa a yammacin jiya asabar  sojojin kasar saudiya sun kai hari kan fararen hula a birnin sana’a na kasar yamen kuma akalla ya kashe mutane 22 mafi yawancinsu mata ne da yara kanana yayin da wasu da dama kuma suka jikkata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted