Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya jaddada game da mihummanci sanya hannun jari da kuma hadin guiwa a iyakoki, a matsayin

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya jaddada game da mihummanci sanya hannun jari da kuma hadin guiwa a iyakoki, a matsayin abubuwan da ya fi mayar da hanakli akai a lokacin ganawarsa da shugaban kasar iraki Abdul latif rashid a gefen taron kasa da kasa na zaman lafiya a kasar Turkmenistan

Tehran da Bagadaza sun dauki hadin guiwa a matsayin babban ginshikin zaman lafiya a yankin da kuma kariya daga tsangwama daga kasashen ketare  musamman Amurka da Isra’ila wadanda ke neman raba kan kasashen musulmi da kuma kawo cikas ga hadin guiwar tattalin arziki da siysa.

Ana shi bangaren shugaban kasar Iraqi ya fadi cewa iran itace makwabciya mafi muhimmanci don muna da alakar tsaro mai karfi, don haka iraki ba za ta taba mantawa da irin goyon bayan da iran take bata ba.

Gwamantin sahyuniya itace tushen haifar da rashin tsaro a yanki ba wai a bangaren hare-haren soji ba kawai , har ma a bangaren kawo cikas din tattalin arziki tsakanin kasashen makwabta. Daga karshe yayi kira da akara fadada dangantakar tsaro da tattalin arziki, manasa’antu, domin duk wani nuna kiyayya ga iran kamar nuna kiyayya ce ga Iraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted