Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Mallakar Mashigar Ruwan Hormuz

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran yana jawabi ga Trump cewa: Mashigar Hormuz ta kasance, kuma ba zata gushe ba tana ci gaba da kasancewa mallakin

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran yana jawabi ga Trump cewa: Mashigar Hormuz ta kasance, kuma ba zata gushe ba tana ci gaba da kasancewa mallakin Iran

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kazem Gharibabadi, wanda ke mayar da martani ga ikirarin Shugaban Amurka Donald Trump game da Mashigar Ruwa ta Hormuz, ya tabbatar da cewa: Mashigar ruwan ta kasance, kuma za ta ci gaba da kasancewa, mallakin Iran.

Gharibabadi ya rubuta a dandalin X cewa: “Trump ya ce nan ba da jimawa ba zai ayyana Mashigar Ruwan ta Hormuz a matsayin mallakin Amurka, bayan murkushe Iran!”

Mataimakin Ministan Harkokin Waje ya bayyana cewa ba za a iya canja sunan Mashigar Ruwa ta Hormuz ta hanyar hare-haren jiragen sama, umarni, ko kuma jawabin zaɓe ba.

Ya ci gaba da cewa, “Iran ba ta jin tsoron barazana, kuma ba ta jin tsoron nuna ƙarfi.”

Gharibabadi ya jaddada: “Ku yarda da wannan gaskiyar sau ɗaya: Kun sha kashi tare da fuskantar wahala sosai a manyan neman nasarar mummunar maufarku. Mashigar Ruwa ta Hormuz ta kasance, kuma za ta ci gaba da kasancewa, mallakin Iran.” Za a rufe wannan mashigar ruwa kuma a buɗe ta ne kawai da umarnin Iran, kuma Iran za ta ci gaba da sanya shingen muddin kun ƙi amincewa da gaskiyar gazawarku kuma kuka fake a bayan ruɗani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted