Shugaban kasar Rasha ya yi magana game da nasarar da kasarsa take samu a yakinta da Ukraine
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da cewa: Kasarsa a shirye take ta gudanar da tattaunawa don kawo karshen yakin Ukraine, amma ya jaddada cewa: Rasha ba za ta yi shawarwari da shugabannin da ke Mulki a birnin Kyiv fadar mulkin Ukraine ba.
A ranar Talata bayan halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a Kyrgyzstan, Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce: Moscow ta kasance a shirye don tattaunawa don kawo karshen yaki da Ukraine da kuma cimma zaman lafiya mai dorewa.
Yayin da yake amincewa da yiwuwar gudanar da tattaunawar tsakanin kasashen biyu, Putin ya yi magana daga wani matsayi mai karfi, yana mai tabbatar da fifikon sojojin Moscow da kuma ikirarin cewa: Rasha ce ke cin galaba a yakin. Kuma ya jaddada matsayinsa na kin amincewa da yin shawarwari da shugabannin Ukraine na yanzu, wadanda ya bayyana a matsayin ‘yan ta’adda.”