Iran Da Rasha Sun Sha Alwashin Tunkarar Matakin Amurka

iran da rasha sun sha alwashin tunkarar takunkumin amurka

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan yace kasar Amurka bata da wani hakki da doka ta bata da za ta sanyawa iran takunkumi kan kasar Iran, ya jaddada cewa Tehran da mosko za su yi aiki tare domin tunkarar matakin nuna  wariya na kasar Amurka.

Pezeshkiyan yayi wadannan bayanan ne a yau talata a lokacin ganawarsa da shugaban kasar rasha Viladmir putin a gefen taron kungiyar hadin kai ta kasashen shangai SCO da ake yi a birnin Bishkek na kasar kyrgystan, kuma ya jinjinawa putin game da goyon bayan da kasar rasha take bawa iran, yace manyan kasashe ba za su iya amfani da karfin soji da na siyasa ba don aikata ayyukan ta’addanci ba tare da yin watsi da kokin kasa da kasa ba.

Haka zalika yace mun jinjinawa kasar rasha game da goyon bayan da take bawa iran , kuma ya bayyana  dangantakar dake tsakani mosko da Tehran a matsayin wadda ta wuce hadin guiwa na yau da kullum tsakanin kasashen biyu .

A nasa bangaren putin ya bayyana goyon bayansa ga alummar kasar iran adaidai lokacin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hari kan kasar Iran, ya jaddada cewa Mosko za ta ci gaba da dangantakar tattalin arziki da kasuwanci dake tsakaninta da Tehran duk da takaddamar siyasa da ta soji da ake ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted