EFCC Ta Kori Ma’aikatanta Sama Da 40 Bisa Zargin Cin Hanci

maaikata 40 sun rasa aiki a efcc saboda cin hanci da rashawa

Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Kasa a Najeriya EFCC, ta kori ma’aikatanta sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata, sakamakon zargin cin hanci da rashawa.

Hukumar ta ce an kori ma’aikatan ne saboda hannu da suke da shi wajen zargin aikata cin hanci da rashawa da kuma almundahana ta kudi, lamarin da ka iya bata sunan hukumar.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, wanda ya bayyana hakan a Abuja yayin ganawa da shugabannin kafafen yada labarai da sauran ƴan jarida, ya ce sama da biyar daga cikin ma’aikatan da aka kora a halin yanzu an gurfanar da su a gaban kotu.

Haka nan shugaban hukumar ta EFCC, ya ce sun samu nasarar hukunta mutane dubu 10 da 872, tare da kwato kudade da yawansu ya haura Naira tiriliyan daya tare da tarin kadarori, tsakanin watan Oktoban 2023 zuwa Yulin 2026.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted