Sakataren Sojin Amurka Ya yi Murabus Daga Mukaminsa

matsala a rudunar sojin Amurka ta sa sakataren sojin amurka yayi murabus

Rundunar sojin Amurka tana fuskantar rudani ta shugabancin inda sakaraten soji Dan Driscoll ya mika takardar murabus dinsa adaidai lokacin da suke takaddama da ministan yaki Amurka Pete Hegseth kan matsalar cikin gida suke fuskanta

Wadannan matsaloli suna zuwa ne bayan da kasar Amurka ta shiga wata na 7 tana yaki mafi tsada da kasar iran, da ya sa sojojin suka kasance ba tare da shugabanci na dindindin na farar hula ko kuma na dindindin a wani mayuwacin hali ba,

Dubun dubatan sojojin Amurka aka tura cikin yakin na watanni 7 da iran, wanda bai yi nasara ba kuma ya jawo mummunan asarar tarin makamai masu yawa, yanzu haka sojojin suna aiki ba tare da sakataren farar hula na dindindin ko babban hafsan soja mai kayan soja ba.

Driscoll tsohon soja ne wanda yayi aiki a Iraki , ya sami kariya daga kisan gilla hegseth saboda kusancinsa na kud da kud da mataimakin shugaban Amurka JD Vance, duk da haka jami’ai sun lura cewa Hegseth ya dauki Driscol a matsayin barazana ga gwamnati kuma ya dade yana neman a sauke shi

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted