Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Berri ya bayyana matukar adawarsa game da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Berut da gwamnatin yahudawan sahyuniya, kuma yayi gargadi game da matsalar dake tattare da tattaunawa da Isra’ila kai tsaye adaidai lokacin da isra’ila take kaddamar da hare hare a kudancin labanon
Nabi birri yayi wannan kalaman ne a wajen bikin cika shekaru 48 da bacewar babban malami kuma jagoran yan shi’a kuma shugaban kungiyar Amal imam musa Al-sadar tare da abokan tafiyarsa guda 2. kuma ya yi ishara da cewa fadin yankin kasar labanon da Isra’ila ta mamaye ya bunkasa ne bayan tattaunawa sau 7 da kuma ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila take yi a kudancin labanon .
A ranar 26 ga watan yuni ne kasar labanon da isra’ila suka rattaba hannu da aka tsara za ta janye sojojinta daga kudancin labanon da ta mamaye sannu a hankali tare da maye gurbinsu da sojojin kasar labanon , sai dai tun 2 ga watana maris isra’ila ta ci gaba da kai hare-harenta a kudancin kasar da yayayi sanadiyar mutuwar muta 4000 tare da jikkata mutane 12000, gwamnatin labanon ta rawaito cewa akalla mutane miliyon daya kuma suka bace daga gidajensu