Shugabannin kasashen kungiyar hadin guiwa ta Shangai SCO sun yi tir da hare – haren da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan kasar Iran, kuma sun bayyana wannan mataki matsayin barazanar ga zaman lafiya da tsaro na duniya.
Taron na beshkek yayi bayanin cewa matakin da mambobin kungiyar suka dauka yayi tir da matakin soji da Amurka da Isra’ila suka dauka kan kasar iran, wanda ya jawo asarar rayukan fararen hula da kuma mummunan barna ga tattalin arziki
An gudanar da taron kolin ne a babban birnin kasar Kyrgystan na bikin cika shekaru 25 da kafa kungiyar yankin , kuma ya nuna irin tasirin da ta yi a matsayin wani babban nauyi ga cibiyoyin duniya da kasashen yamme suka mamayeta, Daga cikin muhimman abubuwa da bayanin bayan taro da aka fitar ya kunsa shi ne kafa cibiyar hadin guiwa don fuskantar kalubale da barazanar da mambobin kungiyar ta SCO suke fuskanta, da kuma mataken da zasu dauka na shekara ta 2026 zuwa 2030 na bunakasa mashigar ruwa da cibiyoyin samar da muhimman abubuwa a fadin yankin.