Saudiyya Ta Yi Allah Wadai Da Kutsen Isra’ila A Masallacin Al-Aqsa

Saudiyya ta bi sahun kasashen dake Allah wadai da kutsen da wasu yahudawa sukayi a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke Kudus tare da gudanar da

Saudiyya ta bi sahun kasashen dake Allah wadai da kutsen da wasu yahudawa sukayi a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke Kudus tare da gudanar da ibadarsu a ciki.

Masarautar ta bayyana kutsen a matsayin harin da aka kai kan haramin masallacin na Al-Aqsa, tana mai watsi da duk wani yunkuri da zai shafi tarihi da dokokin shari’a da suka shafi wurin.

Tsohon birnin na Kudus, yana dauke da wurin ibada na uku mafi tsarki na musulmi, wato Masallacin Al-Aqsa, kuma yana da matsayi a addinin Yahudanci.

A karkashin dokokin da aka cimma na shekaru da yawa tsakanin musulmi, Isra’ila ta ba Yahudawa damar ziyarta wurin amma su guji yin addu’o’i.

Qatar ma ta yi Allah-wadai da kutsen yahudawan a Masallacin na a Al-Aqsa.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta ce matakin da yahudawab suka dauka ya keta dokokin kasa da kasa”.

Tunda farko rahotanni sun ce, wasu ‘yan Isra’ila da dama sun dauki hoton bidiyo suna kan hanyarsu ta shiga harabar masallacin na Al-Aqsa a jiya Lahadi, a yayin bikinsu na Hanukkah da ke gudana.

Shi ma ministan tsaron Isra’ila mai tsatsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir ya kara yawan sojojin Isra’ila a kewayen Masallacin a ‘yan kwanakin nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments