Khatam Al-Anbiya Ta Ce: Iran Ce Ke Da Iko Da Mashigar Hormuz

Kakakin Rundunar Khatam al-Anbiya (SAW) ya bayyana cewa: Babu wani jirgi da zai iya ratsawa ta mashigar Hormuz ba tare da izinin Iran ba Kakakin

Kakakin Rundunar Khatam al-Anbiya (SAW) ya bayyana cewa: Babu wani jirgi da zai iya ratsawa ta mashigar Hormuz ba tare da izinin Iran ba

Kakakin Rundunar Khatam al-Anbiya (SAW) Al-Muqaddi Ibrahim Zulfiqari, ya bayyana cewa: Da’awar da Amurka ke yi wa jiragen ruwa na shigewa ta hanyar mashigar Hormuz wani abu ne da ke nuna zaluncin Amurka. Kuma ba zai yiwu jirgin ruwa ya gudanar da tafiye-tafiye ta mashigar Hormuz ba tare da izini da iko daga Iran ba.

Kuma ya ƙara a cikin saƙon cewa: Ikirarin da Amurka ke yi marar tushe game da wucewar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz – wanda ke nuna halin damuwa da rashin kwarewa na rundunar sojin Amurka- ba komai ba ne face ƙarya.

Kakakin ya jaddada cewa: Mashigar Hormuz, kamar baya ne, tana ƙarƙashin cikakken iko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma jiragen ruwan kasuwanci da jiragen ruwa masu ɗaukar mai, ba za su taba samun wucewa cikin aminci da tsaro ba ta mashigar Hormuz ba tare da izini da amincewa daga rundunar sojojin Iran masu ƙarfi ba.

Ya ci gaba da bayyana cewa: Rundunar Sojin Amurka ‘yar ta’adda tun baya har zuwa yanzu ta fahimci juriya da jarumtakar al’ummar Iran ƙarƙashin jagorancin rundunar sojin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted