Jaridar Washington post ta kasar Amurka ta bada labarin cewa, yakin Amurka da Iran ya lakume jiragen yakin Amurka samfurin MQ-9, guda 45, wanda kuma shi ne kimani kashi 1/4 na yawan irin wadan nan jirage masu tsada wanda Amurka take da su.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Jaridar Washington Post na cewa, kimar wadan nan jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa ya kai dalar Amurka billion 1.3 na dalar Amurka.
Wata majiya a ma’aikatar yakin Amurka ta shaidawa Washington post kan cewa wadan nan jirage masu tsada kimani 185 ma’aikatar Pentagon take da su, amma a cikin kwanaki 40 da Amurka ta shiga yaki da Iran an rasa 45 daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa MQ-9 yana daga cikin jiragen yakin Amurka wadanda ake sarrafasu daga nesa, masu leken asiri ko kuma tare da kai hare hare a wasu lokuta mafi inganci da sojojin Amurka suke da su. Kuma kimar ko wanne daga cikinsu, ya danganci irin kayan aiki da aka dora sama, ya kai tsakanin dalar Amurka miliyon 30 zuwa 50..
Don haka kimar wadanda Iran ta kakkabo ko Amurka ta rasasu a yakin Iran ya kai dalar Amurka billion 1.3.
Iran ta kakkabo mafi yawan jiragen ne a kusa da mashigar ruwa ta Hurmuz, kuma mai yuwa rashin sauri mai yawa dakuma shawagi kasa kasa ne ya sa suke da saukin kakkabowa a wajen Iran da Yemen da kuma kasar Iraki.