Abbas Araqchi Ya Mayar Da Martani Ga Kasar Faransa

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana kiran Faransa ga duniya game da kare hakkin dan adam a matsayin munafunci bayyananne Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana kiran Faransa ga duniya game da kare hakkin dan adam a matsayin munafunci bayyananne

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya ce, a martanin da ya mayar wa Ministan Harkokin Wajen Faransa John Noel Barro, cewa ya kamata kasashe kamar Faransa su daina yi wa duniya kira game da ‘yancin ɗan adam da kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa, yana mai kiran wannan a matsayin munafunci bayyananne da abin kunya.

Araqchi ya rubuta a cikin wani jawabi a dandalin X, a yau Alhamis, don mayar da martani ga Ministan Harkokin Wajen Faransa John Noel Barrow: Dole ne ƙasashe kamar Faransa su daina yi wa duniya kira game da haƙƙin ɗan adam da kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa, domin hakan munafunci ne bayyananne.

Ya ƙara da cewa: Goyon bayan da suke bai wa Haramtacciyar Kasar Isra’ila a kan yakin Gaza, da kuma hare-haren da ake kai wa Iran, ya lalata duk wani fifikon ɗabi’a da suke tunanin suna da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted