Iran Ta Lalata Shirin Siriya Na Yakar Hizbullah A Lebanon

Wata kafar yada labarai U-News ya bada labarin cewa JMI ce ta lalata shirin shugaban kasar Amurka Donal trump na tura sojojin kasar Siriya zuwa

Wata kafar yada labarai U-News ya bada labarin cewa JMI ce ta lalata shirin shugaban kasar Amurka Donal trump na tura sojojin kasar Siriya zuwa cikin kasar Lebanon don kwance damarar kungiyar Hizbullah da ke kudancin kasar.

Tashar talabijan ta Al-Maydeen ta kasar Lebanon ta nakalto U-News na cewa gwamnatin kasar Iran ta fadawa shuwagabannin kasashen Turkiyya, Iraki Qatar da kuma Saudia kan cewa idan sun kuskura sun tura sojojin Siriya cikin kasar Lebanon to kuwa Iran zata cilla makamai masu linzami a zagaye na farko har guda 100 kan kasar Siriya, kuma fadojin shugaban kasar ta Siriya na daga cikin bararsu ta farko.

Banda haka, iran ta sahida masu cewa sai ta samarda yan adawa a kasar Siriya wadanda zasu kifar da gwamnatin Shugab Ahmad Shar’a.

Labarin ya kara da cewa, kafin haka shugaban Amurka Donal Trump ya bukace Ahmad Shar shugaban kasar Siriya ya taimakawa HKI su kwamce damarar kungiyar Hizbulla a kudancin kasar Lebanon wanda zai bawa HKI damar mamayar kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted