Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran yana bayyana wa Amurka cewa: Hakika ta tafka babban kuskure kan batun mashigar Hormuz
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi, yayin da yake magana game da raunin leƙen asirin Amurka da kuma rashin kimarsa, ya ɗauki yaƙin da aka yi da Iran a matsayin misali bayyananne na waɗannan kurakuran, kuma ya ce wa hukumomin Amurka: “Abin da ya fi labaran karya muni shi ne bayanan karya da suke fitarwa– Ya kamata su kula.
Araqchi ya rubuta a yau Alhamis a cikin wata sanarwa a kan dandamalin “X” da yake Magana da hukumomin Amurka cewa: “Amurka ta daɗe tana fama da kurakurai masu yawa game da asalin raunin leƙen asiri.” Kuma yaƙin da ta daura kan Iran misali ne bayyananne na hakan. A yau ta yi babban kuskure a hasashen da ta yi game da mashigar Hormuz.
Araqchi ya ci gaba da cewa: Abin da ya fi muni daga labaran karya da Amurka ke samu, shi ne bayanai marasa tushe da take dogaro da su a matsayin hujja.
Ya jaddada cewa: Allah mai girma ne, da ya fi kowane girma a kan doron kasa, don haka Iran ta dogara ne ga Allah Maɗaukaki.