Morocco Ta Zama Wurin Jarraba Makamai Masu Linzami Na HKI

Wasu kafafen yada labarai na harshen ‘Ibranci’ ya fallasa labarin da ke cewa Amurka da HKI sun maida kasar Morocco a matsayin wurin gwada makamansu

Wasu kafafen yada labarai na harshen ‘Ibranci’ ya fallasa labarin da ke cewa Amurka da HKI sun maida kasar Morocco a matsayin wurin gwada makamansu masu linzami.

Sashen yarin ‘ibranci’ na kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wata kafar labarai ta HKI na cewa, Amurka da HKI sun gwada makamansu masu linzami samfurin Kuruz a cikin kasar Morocco.

Labarin ya kara da cewa kamfanin kera makamai na Covent Industries  mallakin Amurka da HKI sun gwada makaman da suka kera mai suna Anthem a wani yankin da ake kira Tantan da ke kudancin kasar Morocco a ranar 6 ga watan Augusta da muke ciki.

Labarin ya kara da cewa, saboda yarjeniyar ‘Ibrahimi’ da ke tsakanin morocco da hki kasashen suka aiwatar da wadan nan gwaje gwajen makamansu a kasar Morocco. Sun kuma gwada makaman su daban daban a wani atisayen soje tare da sojojin kasar ta Morocco.

Labarin ya kara da cewa abisa yarjeniyar ‘Ibaraham’ a duk lokacinda Amurla da HKI suka nemi wurin gwada makamansu a cikin kwanaki 30 dukkan kasashen da suke cikin wannan yarjeniyar zasu samar da wuraren gwajinsu a kasashensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted