Iran: Amurka Ce Da Alhakin Gurbatan Tsibirin Qeshm Da Mai

Mataimakin ministan harkokin waje na kasar a cikin al-amuran sharia da kuma kasashen waje, Iran Kazem Garib Abadi ya bayyana cewa gurbatan Iran’s Deputy Foreign

Mataimakin ministan harkokin waje na kasar a cikin al-amuran sharia da kuma kasashen waje, Iran Kazem Garib Abadi ya bayyana cewa gurbatan Iran’s Deputy Foreign Minister for Legal and International Affairs Kazem ruwan tekun farisa a kusa da tsibirin Qeshm saboda hare haren da Amurka da HKI suka kai kan cibiyoyin man fetur a bakin ruwan mashigar ruwa ta Hurmuz ne.

Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar Iran ya nakalto Garib Abadi yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa hare haren da jiragen yakin Amurka da HKI da kuma kawayensu suka kai kan cibiyoyin man fetur a bakin ruwa tekun farisa ne suka haddasa gurbatan ruwan tekun, kuma zai iya zama hatsari ga rayuwar dabbobin ruwa a yankin.

Kafin haka dai, Habib Masihi Taziani darakta mai kula da al-amuran yanayi a lardin Hurmuzgan ya bada labarin samuwar gurbatan ruwan tekun farisa a kudancin tsibirin Qeshm, da kuma kokarinda ma’aikatansa suka yi na tsabatace ruwan.

Tazia ni ya kara da cewa sun yi amfani da kayakin aiki na musamman don tsabtace ruwan tekun farisa a kudancin tsibirin Qeshm da kayaki aini na musamman don yin haka. Yace gurbataccen yashin da suke bakin ruwan, suma an kwacesu ta yanda ba zai cutar da mutane ko dabbobin ruwa nan gab aba.

Jami’an hukumar kula da yanayi a yankin sun bada rahoton gurbatan ruwa tekun farisa a garuruwa nab akin ruwa a kudancin kasar wadanda suka hada da tsibirin Lavan Bandar Maqam, Qeshm, Larak, Hengam da kuma tsibirin Hormuz.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted