Iran: Yakamata BRICS Ta Bude Kafar Musayar Kudade

Gwamnatin JMI ta gabatar da shawara ga kasashen kungiyar raya tattalin arziki ta BRICS na a samar da wa nit sarin sadarwa na bai daya

Gwamnatin JMI ta gabatar da shawara ga kasashen kungiyar raya tattalin arziki ta BRICS na a samar da wa nit sarin sadarwa na bai daya tsakanin kasashen kungiyar wanda zai kawo sauki wajen hada hadar kudade da kuma harkokin kasuwanci mai sauki tsakanin kasashen kungiyar.

Kamfanin dillancin labaran Mehrnes na kasar Iran ya nakalto gwamnan babban bankin Iran Dr Abdunnasir Himmati yana fadar haka a jiya Alhamis a rana ta biyu na taron gwamnonin babbam bankunan kasashen kungiyar wanda aka kammala a kasar India.

Dr Himmati ya kara da cewa, samar da irin wannan tsarin zai taimkawa kasashen kungiyar musayar kudade da kasashensu, kuma zai rahe kudaden da za’a kashe wajen aiwatar da kasuwanci tsakaninsu. Ya kuma rage dogaron da kasashen zasu yi da wasu kafafen don irin wadan nan harkokin kasuwanci ko musayar kudade.  Har’ila yau hakan zai kara sauri da amincin hulda tsakanin kasashen da kuma kaucewa duk wata cutar da wasu zasu iya yiwa kasashen kungiyar.

Ya ce, idan kasashen sun amince Iran tana da wasu hanyoyi na misalign yanda za’a samar da Irin wannan tsarin.

Himmati yana kasar India tare da tawaga mai yawa daga gwamnatin kasar Iran don halattan taro na farko kan harkokin kudade na kungiyar BRICS a birnin New Delhi na kasar India.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted