Iran Ta Bukaci Kwance Damarar Makaman Nukliya A Duniya

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a Geneva ya yi kira ga kasashen duniya su fara tattaunawa don kwance damarar kasashen wadanda suka mallaki makaman

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a Geneva ya yi kira ga kasashen duniya su fara tattaunawa don kwance damarar kasashen wadanda suka mallaki makaman nukliya a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Mohammad Hossain Sayyadnejad yana fadar haka a taron kwace damarar makaman nukliya wanda aka gudanar a birnin Geneva a jiya Alhamis 6 ga watan Augusta da muke ciki.

Sayyadnejad ya kara da cewa batun kwance damarar kasashen da suka mallaki makaman nukliya ba siyasa bace, dokokin kasa da kasa ne suke bukatar hakan.  Yace dole ne wadan nan kasashen sun kwance  damarar makamansu na Nukliya, kuma doole ne kawo karshen makaman nukliyar da HKI ta mallaka, don kawo karshen makaman gaba daya a yankin yammacin Asiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted