Kakakin Ma’ikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Bayanin haɗin gwiwa tsakanin Iran da Oman game da mashigar tekun Hormuz yana gab da fitowa
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce: Hukumomin da suka dace sun yi nazari kan fannoni daban-daban na fasaha, shari’a, tsaro da muhalli na tattaunawar da ke tsakanin Iran da Oman don tantance hanya mai aminci don wucewar jirage ruwa masu zirga-zirgar kasuwanci a Mashigar tekun Hormuz suna gab da kammala ayyukansu.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, a martanin da ya mayar kan tambayoyin ‘yan jarida game da wasu rahotanni da kafofin watsa labarai na yanki da na yamma suka buga game da tattaunawar tsakanin Iran da Oman, ya ce tattaunawar da ke tsakanin kasashen biyu, a matsayin kasashen da ke gabar tekun Mashigar Hormuz, ta shafe watanni biyu tana gudana da nufin tantance hanya mai aminci ga jigilar kayayyaki na kasuwanci, yana mai nuna cewa hukumomin da suka dace sun yi nazari kan fannoni daban-daban na fasaha, shari’a, tsaro da muhalli na wannan hanyar suna ci gaba da ayyukansu.
Isma’il Baqa’i ya kuma tabbatar da cewa: Hanyar tattaunawar tsakanin kasashen biyu “na kwararru” ce kuma “tana ci gaba Shirin bayyana nan gaba”, yana mai bayyana cewa daidaiton yanayin hanyar da bangarorin ke so ya kai ga fahimta tsakaninsu. Ya ƙara da cewa idan wasu ɓangarori na uku ba su hana wannan hanya ba, sanarwar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, wadda za ta haɗa da manyan abubuwan da aka tattauna da kuma abubuwan da aka cimma, a halin yanzu ana ci gaba da bitarsu da kuma tsara su a matsayi na ƙarshe.