Limaminmasallacin jumma’a a nan Tehran ya godewa mutanen kasar Iraki kan kekyawar bakoncin da suka yiwa Iraniyawa da mutanen sauran kasashen duniya a juyayin 40 na Imam Alhussain (a).
Kamfanin dillacin labaran mehr News na kasar Iran ya nakalto hujjatul Islam Jawad Ali Akbari yana fadar haka a khudubobinsa na sallar jumma’a a nan Tehran ya kuma kara da cewa,
Juyayin 40 na Imam Hussain(a) a bana na musamman ne saboda halin da ake ciki a yankin da kuma duniya gaba daya. Da farko a cikin wannan shekarar ne aka dorawa JMI yaki, sannan a cikinta ne Imam Jagora Shahid yaya shahada, sannan miliyoyin mutanen Iraki suka yi masa rakiya a wurare masu tsarki na kasar.
Sannan daga baya aka gudanar da makokin 40 na Imam Hussain (a) wanda miliyoyin mutanen daga kasar Iran da sauran kasashen duniya suka sake zuwa kasar Iraki don juyayin.
Yace muna godewa mutanen kasar Iraki, da gwamnati da kuma manya manyan malamansu wadanda suka nunawa duniya kan cewa su sun iya daukar bakwanci. Da kuma girmama baki. Da karshe limamin ya roki All..T ya yi albarka wa mutanen kasar Iraki ya kuma daukakasu duniya da lahira.
Daga karshe ya yi tsokaci dangane da sanya mayafi ko hijabi ga mata, inda ya bayyana cewa umurnin All..ne sannan an gajeshi daga Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s).