IRGC Sun Baje Makaman Amurka Da HKI Da Suka Kakkabo

IRGC Sun Baje Burbushin Makaman Amurka Da HKI Da Suka Kakkabo A Yakin Kwanaki 40 Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran (IRGC)

IRGC Sun Baje Burbushin Makaman Amurka Da HKI Da Suka Kakkabo A Yakin Kwanaki 40

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran (IRGC) sun baje wace tarkacen makamai da jiragen yakin Amurka da HKI wadanda suka kakkabo a yakin kwanaki 40 da suka dorawa kasar daga cikin har da na jirgin yaki samfurin F-35 wanda suka kakkaboshi a kudancin kasar.

Dakarun sararin samaniya na IRGC ne suka kakkabo jirgin wanda Amurka, kafin haka tana tutiya kan cewa ba wanda ya isa ya ganshi ma, ballantana ya kakkaboshi a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran da kuma hukumar tashoshin radio da talabijan na kasar sun nuna tarkace da dama na ragowa jiragen yaki da makaman da suka kakkabo daga cikin har da kujera da rigar matukan jirgin na F-35, wanda suka cilla kansu waje a lokacinda suka gano cewa an kakkabo jingin nasu.

Saurin tarkacen makaman Amurka da HKI sun hada da makamai masu linzami na cruse da sauransu.

Janar Hossin Mohebbi kakakin dakarun IRGC ya bayyana cewa, bayan yakin kwanaki 12 ne, wato a ranar 13 ga watan yunin shekara ta 2025, rundunar ta kare sararin samaniyar kasar ta ga yakamata da samar da garkuwa wacce zata kakkabo jiragen yakin F-35, kuma sun sami nasarar kera shi sannan suka yi amfani da shi wajen kakkabu shi a yakin kwanaki 40.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted