Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara a kan tsaro ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata taba amincewa Amurka ko wata kasa ta bude wata hanyar zirga zirgan jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hurmuz ba, ban da wanda JMI ta ayyana.
Mehsin Rezai, ya bayyana haka ne a daren jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, idan Amurka ta yi kuskuren samar da wata hanyar zirga zirga daga kudancin Hurmuz zata gamu da fushin sojojin Iran, kuma dole ne Washington ta amince da ikon JMI a kan wannan mashigar ta kuma sauya halayenta dangane da JMI.
A cikin yan kwanakin da suka gabata ne aka nada Rezai a matsayin babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a JMI.
Mashigar ruwa ta Hurmuz kuma ta kasasnce a bude kafin yakin da Amurka da HKI suka dorawa JMI, a farkon wannan shekarar, kuma tana da matukar muhimmanci a fagen tattalin arziki da kuma makamashin ga dukkan kasashen duniya.