Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa, hadin kai tsakanin kasashen yankin da kuma tsakanin mutanen kasar Iran sun taimakawa kasar wajen kaucewa tasirin takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka suka dorawa kasar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran yana nakalto shugaban kasar yana fadar haka a wani jawabi na musamman da yayiwa mutanen kasar a dai dai lokacinda yake cika shekaru biyu da kama aiki a matsayin shugaban kasa.
Shugaba ya kara da cewa karancin kudaden waje ya tilastawa kasar Iran aiwatar da kasuwanci nau’in bani gishiri in baka manda wato ‘Trade by Barter” da kasashen yankin.
Yace kasashen yankin sun taimakawa kasar wajen yakar yan ta’adda wadanda suke son shiga kasar Iran ta kasashensu, tare da taimakon Amurka da HKI. Saboda wannan taimakon sun kasa shiga kasar Iran musamman a lokacin yaki na baya bayan nan.
Daga karshe shugaba Pezeshkiyan ya yabawa Jagora Shahid Ali Khaminai (q) wanda ya tsara dukkan wadannan al-amura, kuma shi ne makoma ga gwamnatin kasar a duk lokacinda suka shiga matsaloli.