A Faransa dubban mutane sun yi zanga-zanga a fadin kasar a mako na shida a jere kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin makamashi, rashin daidaito, da kuma tabarbarewar ayyukan gwamnati.
Masu shirya zanga-zangar sun kiyasta cewa mutane 150,000 ne suka halarci zanga-zangar a duk fadin kasar jiya Asabar.
An gudanar da zanga-zangar a biranen da suka hada da Lille, Marseille, da kuma Lyon.
Rahotanni sun ce an yi arangama a wasu wurare, inda ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Faransa ta ba da rahoton kama mutane 144 zuwa yammacin jiya.
Tunda farko dai Hukumomi a Faransa sun ce an jibge jami’an tsaro 70,000 gabanin sabuwar zanga zangar ta tsadar rayuwa da .
Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Laurent Nuñez ya sanar cewa an tura jami’an ‘yan sanda da na Jandarma 70,000 a fadin kasar a ranar Asabar, don tunkarar zanga-zangar.
Jerin kungiyoyi a faransa sun shiga zanga zangar tsadar rayuwa da hauhawan farashin makamashi wacce ta samo asali daga fishin daliban makarantun sakandare dake zargin gwamnati da gazawa wajen warware matsalolin da suka dabaibaiye sha’anin ilimi a kasar.
Zanga zangar ta hada daliban makarantar sakandare da na jami’a, ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu, bisa ga kiran kungiyoyin kwadago na gwamnati.