A cikin wani bayani da kakakin sojin kasar Yamen ya yi birgedier janar yahya Saree ya nuna cewa dakarun sojin kasar yame sun kai hare haren mayar da martani da makami masu linzami na ballistic da kuma jirage marasa matuki a filin saukar jiragen sama na sarki khalid kai tsaye kuma ya jawo dakatar da ayyuka a nan take
Hari na biyu da suka kai kuma ya fada ne kan wani muhimmin bangare a matatar mai ta Aramco a Rabigh inda ya haddasa tashin gobara a bangaren, sai kuma hari na 3 ya nufi sansanin soji na Khamis mushait da sansanin soji na Akafa dake Asir wata maboyar kayyakin soji mai muhimmacni a najran da Jazan duk sun fuskanci hare hare kamar yadda kakakin ya bayyana
Kamar yadda yazo ta bakin dakarun sojin kasar yamen wanann yana zuwa ne a matsayin mayar da martani kan hare haren saudiya a kasar yamen, inda sojojin kasar saudiya suka kaddamar da gwamman hare hare a cikin saoi 24 da suka gabata a birnin sana’a da kuma lardin al-jawf , Taiz, Hajjah , Saada, da kuma Marib, kuma ya kashe tare da jikkata faaren hula, da mata da yara. ya zuwa yanzu saudiya ta kashe mutane 1576 da basu san hawa ba balle sauka a kasar yamen