Pakistan, Turkiya Da Saudiyya Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniayr Tsaro

Kamfanin dillancin "Reuters" ya nakalto cewa ayau Juma'a ne kasashen uku na Pakistan, Turkiya da Saudiyya za su rattaba hannu akan yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu
Tutocin kasashe uku

Kamfanin dillancin “Reuters” ya nakalto cewa ayau Juma’a ne kasashen uku na Pakistan, Turkiya da Saudiyya za su rattaba hannu akan yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu a birnin Jidda na kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labarun na ‘reuters’ ya nakalto majiyar kasashen yankin suna tabbatar da cewa ayau juma’a ne za a rattaba akan yarjejeniyar tsaron.

Shi kuwa kamfanin dillancin labarun ” AFP” ya ce; shugabannin gwamnatocin kasashen uku ne za su halarci rattaba hannun da su ne; Muhammad Bin Salman na Saudiyya, Rajab Tayyib Urdugan na Turkiya sai kuma Shahbaz Sharif na Pakistan.

Majiyar ta kuma kara da cewa; kasashen sun dade suna tattauna wannan batu, sai dai sauye-sauyen siyasa da suke faruwa a cikin wannan ne su ka sa aka karato da rattaba hannu a kusa.

Tun a jiya Alhamis ne dai Fira ministan kasar Pakitsan sharif da babban hafsan hafsoshin sojan kasar Asim Munir su ka isa Saudiyya, yayin da ake sa ran cewa a yau Juma’a ne, Shugaban kasar Turkiya zai isa.

Dama dai kasashen Saudiyya da Pakistan suna da yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu wacce aka sanar da ita a 2025.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted