Norway Ta Ce: Kaddamar Da Yaki Kan Iran Baya Kan Doka

Ministan Harkokin Wajen Norway ya bayyana cewa: Yaƙin Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kaddamar kan Iran, ya yi hannun riga da dokokin ƙasa da

Ministan Harkokin Wajen Norway ya bayyana cewa: Yaƙin Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kaddamar kan Iran, ya yi hannun riga da dokokin ƙasa da ƙasa

Ministan Harkokin Wajen Norway Esben Bart ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kamar sauran kasashen duniya, tana da ‘yancin kare kanta, yana mai cewa yakin da Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka fara a ranar 28 ga Fabrairu kan Iran ya saba wa dukkan dokokin kasa da kasa.

Ministan Norway ya bayyana goyon bayansa ga kokarin Pakistan na taimakawa zaman lafiya a yankin ta hanyar shiga tsakani, yayin da yake magana a ranar Alhamis a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Pakistan a Islamabad.

Ya kara da cewa Norway na daya daga cikin kasashen Yamma na farko da suka bayyana matukar damuwa game da yakin da aka sanya wa Iran, sannan ya ce: Suna daukar yakin Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka daura wa Iran a matsayin wanda ya saba wa dukkan dokokin kasa da kasa.

Kuma ya kara da cewa: Saboda wannan dalili, dokokin kasa da kasa dole ne su hada da dukkan kasashe, ciki har da Iran, wacce ke da ‘yancin kare kanta kamar sauran kasashe a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted