Kungiyar Yaki Da Ta’addanci A Iraki Ta yi Watsi Da Shirin Gwamnati

kungiyar yaki da ta'addanci ta iran ta yi biris da shirin gwmanatin kasar na kwabe dammararsu

Kungiyar yaki da taa’ddanci ta kasar iraki ta yi watsi da bukatar da ministan harkokin wajen kasar yayi Fuad Hussain na nuna amincewa da shirin gwamnati na sanya dukkan makamai su koma karkashin kulawarta a kasar, yace ba su sanya hannu kan wata yarjejeniya ba da gwamnatin bagadad na cewa za ta mika makamanta

Kungiyar Kata’ib sayyidil shuhada a cikin wani bayani da ta fitar ta yi watsi da duk wani bayani da Hussain yayi kuma ta jaddada cewa ba ta bayyana ba, kuma bata amince ba, kuma bata sanya hannun kan komai ba dangane da makamanta

Haka zalika sun yi kira ga jami’an gwamnatin Iraki  da su tabbatar da inganci da kuma daukar nauyi sa’ilin da zasu yi wani bayani ko fitar da wata sanarwa ga alummar kasa, domin kaucewa haifar da rudani ko kuma batar da ra’ayin alumma

a jiya Asabar ce Hussain yace fira ministan kasar Ali al Zaidi ya cimma yarjejeniya da wasu kungiyoyin masu rike da makami guda 4 a kasar game da muhimmacin mayar da dukkan makamai karkashin ikon gwamnati da kuma karfafa ikon dakarun tsaron kasar

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted