Kungiyar Hamas Ta Yi Tir Da Yadda Duniya Ta Yi Shiru Akan Harin Asibitin Al-Shifa

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta yi tir da yadda kungiyoyin kasa da kasa su ka yi shiru akan mummunan halin da asibitin “Al-Shifa’ yake

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta yi tir da yadda kungiyoyin kasa da kasa su ka yi shiru akan mummunan halin da asibitin “Al-Shifa’ yake ciki bayan harin da sojojin HKI su ka kai masa da tafka laifukan yaki a cikinsa.

A wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar a yau Lahadi ta ce har yanzu HKI tana cigaba da tafka laifukan yaki, na yi wa fararen hula kisan kiyashi, da kona musu gidaje, haka kuma barin mutanen yankin Gaza ba tare da abicin ko ruwan sha ba.

Kungiyar ta Hamas ta nuna mamakinta akan yadda kungiyoyin da cibiyoyin da suke a karkashin MDD su ka yi shiru akan ta’asa irin ta ‘yan Nazi da HKI take yi.

Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta bukaci ganin kungiyoyin kasashen musulmi da na larabawa da masu ‘yanci a duniya da su yi duk abinda za su iya yi domin kawo karshen kisan kiyashin da HKI take yi wa mutanen Gaza.

Asibitin Al-Shifa da wasu asibitocin yankin Gaza suna daga cikin wuraren da HKI take kai wa hare-hare tun farkon fara yakin Gaza a watan Oktoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments