194- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikinshirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin siarar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da magana dangane da siyasar Iyalan gidan manzon Allah (s) a gaban irin siyasar Mu’awiya dan Abusufyan da shi da ma’aikatansa a lokacin da al-amuran shugabancin al-ummar Musulmi suka koma hannusa.
A cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku Karin bayan ikan sharuddan da Imam Al-Hassan (a) ya shimfidawa Mu’awaiya dan Abusufyan, kafin ya mika masa ragamar shugabancin al-ummar Musulmi.
Mun fara da aiki da littafin Allah da sunnar manzon Allah (s) a matsayin sharadi na farko wanda Imam Al-Hassan (a) ya fara kawowa, ya shardantawa Mu’awiya dan Abusufyan aiki da littafin Allah da kuma sunnar manzon Allah (s) a cikin shugabancinsa, wannan kuma don ya san cewa Mu’awiya ba zai yi aiki da su ba.
Sannan na biyu kuma ya shardanta masa cewa kada ya nada wani a matsayin magajinsa saboda shugabanci zai koma ga shi Imam Al-hassan (a) a bayansa, ko kuma dan uwana Imam Hussain (a) idan har ba ya duniya. Ko kuma a maida shi shoora a tsakanin musulmi su zami wanda ya dace. Wanda munce Mu’awiya bai yi aiki da wannan sharadin ba.
Sannan ya shardanta masa aminci ga dukkan musulmi, Imam Alhassan (s) ya shardantawa Mu’awiya amintar da dukkan musulmi a ko ina suke a cikin daular musulunci. Sannan ya amintar da mutanen kasar Iraki wadanda suka yakeshi tare da mahaifinsa a Siffin, wanda shima mu’awaiya bai kiyake ba. Bil’hasali ma ya azabtar da mutaken iraki azabtarwann da ba’a taba ganinsa a tarihin bil’adama ba.
Ya shardanta masa cewa kada a kirashi Amirul muminina saboda wannan sunan manzon Allah (s) ne ya kebe Amirul muminina Aliyu dan Abitalib da shi, bai kamata a kira azzalumin sarki da shi ba.
Sannan ya hana shi a yi tsaida shaida a gabansa, saboda bai cancanci a tsaida shaida a gabansa ba, tun da shi azzalumin sarki ne. wannan ya tube shi daga shugabanci al-ummar musulmi duk da cewa a zahiri shi ne shugaba.
Sannan mun yi maganar dakatar da zagin mahaifinsa kuma Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). wanda mu’awiya yaki ki amincewa, har wata rana shi mu’awiya ko daya daga cikin ma’aikatansa ya zagi Amirul muminina (a) a kan mimbarin manzon Allah (s) a Madina sai matarsa Ummu Salma ta ji zagin sai ta daga murya tana cewa me ya sa kuke zagin manzon Allah (s) a kan mimbarinsa ? sai suka bata amsa da cewa ai bas hi muka zaga be Amiyu dan Abitalib ne mukazaga, sai ta ce masu na jimanzon Allah (s) yana cewa wanda ya zagi Aliyu ya zage ni.
Amma wannan bai hanasu ci gaba da zaginsa a kan mimbarorin musulmi ba har zuwa shekara ta 99 ko 100 bayan hijira, sarki umar dan Abdul Azizi ya kawo karshen zagin.
Sannan mun yi maganar aminci ga dukkan musulmi. Imam Al-Hassan (a) ya bukaci Mu’awiya dan Abu sufyan ya tabbatar da amincin dukkan musulmi a ko ina suka a duniya. Musamman amincen mutanen kasar Iraki wadanda suka yake shi tare da mahaifinsa a Siffin. Musamman kuma iyalan gidan manzon Allah (s) Musamman kuma Shi da kaninsa Imam Al-Hussain (s). Amma mu’awiya da ma’aikatansa basu cika go daya daga cikin sharuddan sulhun da da cimma da Imam Al-Hassan (a) ba.
Banda haka Imam Al-Hassan (a) ya damu da shi’ar sa da kuma shi’ar mahaifinsa Amirul muminin (a), saboda kare jininsu ne ya yi sulhu da Mu’awiya dan Abusufyan. Ya jiye masu tsoron abinda zai faru bayan ya mika shugabanci ga Mu’awiya dan Abusufyan. Don haka ne ya kawo shi cikin sharuddan mika masa shugabanci.
Amma mu’awiya bai barsu ba. Mafi munin kissan da yayi wa shi’ar Amirul muminina (a) shi ne kissan da yayiwa Hijiru dan Adiy da sahabbansa.
Mu’awiya ya bukaci daya daga cikin manya-manyan sahabban amirul muminina (a) mutumin Kufa wanda ya kasance shugaba a cikin kabilarsa, kan ya zagi Amirul muminina (a) Hijir ya ki amincewa.
Sai Ziyar dan Abihi ya tura shi Damascus wajen Mu’awiya da shi da dansa da wasu mutanensa. A lokacinda Mu’awiya ya sami labarin isowarsu Dameshi ya sa ce kada a shigo da su cikin gari.
A bukaceshi su la’ani Aliyu dan Abitalib (a), idan sun ki har zuwa Asubaha a kashe su gabadaya. Wasu lamaman tarihi sun ce 7 ne da shi da dansa da wasu yan kabilarsa mutanen Kufa suka ki amincewa su la’ani Aliyu dan Abitalib (a) ma’aikatansa suka haka rami ga ko wanne daga cikinsu, a gabansu suka kuma kashesu suka binne ko wannensu a cikin ramin da suka haka masa.
Wasu malaman sukan kawo abinda wani malami daga cikin malaman shi’a ya ruwaito a lokacinda ya ziyarci kabarin Hijru dan Adiyya da sahabbansa, yana cewa watarana na je ziyarar kabarin Hijru dan Adiy( R) sahabin manzon Allah (s) kuma sahabin Amirul Muminina Aliyu dan Abitalib (a) a wajen birnin Damascus babban birnin kasar Siriya sai na sami wani mutum yana kuka a kan kabarin, sai na tambaye shin a ce: Shin kabarin waje wannan? Sai y ace Kabarin siyyida Hijir dan Adiy ne, sahabin manzon Allah (s), sai nace me ya sameshi, sai yace Sayyida Mu’awiya ne ya kasheshi, saboda yaki ya zagi sayyida Ali (a). Sai malamin ya ce: To kaima Allah ya jikanka. Sai ta tashi ya sai aka tambaye shi me kake nufi Allah ya jikansa? Sai yace, don shi ma baya iya bambamcewa tsakanin sayyidinsa, da wanda ya kashe da wanda aka kashe duk shuwagabanninka ne.
Sannan Imam Al-Hassan ya shardantawa Mu’awiya dan Abu Sufyan ya bashi harajin Doro-Bijard, saboda, a musulunci kudaden da hukuma take karba a wajen mutane, daga cikinsu akwai Zakka ko sadaka, wanda haramun ne ga iyalan gidan manzon Allah (s). Sannan ana kiransa duttin mutane ne, sannan akwai fai’u wanda shi kuma ana samunsa ne daga wuraren da aka samesu ba tare da yaki ba. Wanda shi ya halatta a kasheshi a ko ina, wajen da limami ya ga dama, don haka ne ya zabi harajin wannan wurin don kansu da kuma mabiyansau.
A hadisi manzon Allah (s) yana cewa {An umurce ni, dangane da sadaka (Zakka) in karba daga hannun mawadatanku in maida ita ga talakawansu}
Don haka Imam ya ki ya karba daga kudaden da Mu’awiya yake karba daga mutane da sunaye daban daban, saboda shubhan da ke cikinsa, amma sai ya kebe harajin Doro-Bijard na kasar Farisa saboda tsarkin da ke cikinta. Amma mun bayyana cewa Mu’awiya bai cika ko daya daga cikin alkawulan da ya daukawa Imam Al-Hassan ba.
Sai kuma sharadin rashin tsokana ko zaluntar Iyalan gidan manzon Allah (S), wannan sharidan Imam (a) ya kawo shi ne don ya kunyata Mu’awiya ya kuma bayyanawa mutane hakikansa. Ya san cewa Mu’awiya ne zai kashe shi, shi zai sanya masa guba a cikin abin shansa ya kuma kashe shi.
Ya san cewa, Mu’awiya zai kashe shi da guba, sannan dansa yazidu zai kasheshi kaninsa Imam Hussain a Karbala. Don haka idan mutanen sun ga yayi haka sun san wani matsayi zasu sanya shi. Zai aikata zai sabawa sharadin da Imam Al-Hassan (a) ya shardanta masa.
Da wannan kuma Imam Al-Hassan (a) ya nuna irin baiwar da Allah yayi masu, wato iyalan gidan manzon Allah (a) na iya shugabanci a lokaci da hali mai rikitarwan da al-umma ta fada ciki. Amma ya iya fida da wadan nan tsare-hare na kare al-ummar kakansa manzon Allah (s), a gaban azzaluman sarakuna na lokacin da kuma masu zuwa.
Wasumalaman tarihi sun bayyana cewa sharuddan da Imam Alhassan (a) ya shimfidawa Mu’awiya dan Abusufyan kafin ya mika masa shugabancin al-ummar musulmi, suna daga cikin abubuwan da suka sabbaba faduwar daular Banu Umayya daga baya a hannun yan tawaye wadanda suka taso daga kasar Farisa karkashin shugabancin Abumuslimul Khurasani.
Malaman tarihi sun bayyana cewa, tare da wadan nan sharuddan da ya shimfidawa Mu’awiya dan Abu sufyan bayan ya yaudari mafi yawan rundunarsa, da alkawulan da bai cika masu ba, sannan yaudarar ta isa har zuwa wajen mutane mafi kusa da shi, kamar Abaidullahi dan Abbas wanda ya kasance babban kwamandan sojojinsa kimani 10,000. Wannan ya say a debe kauna daga samun nasara a kan Mu’awiya tare da wadanda suke rage tare da shi.
Sannan al-amari ya kai matsayinda bai amince da mafi yawan sojojinsa ba, saboda tsoron kada su kama shi su mikawa mu’awiya ya kaskanta shi. Wannan da kuma wasu dalilan suka sa Imam Al-Hassan (a) ya zamu sulhuntawa da Mu’awiya ya kuma mika masa al-amuran shugabancin al-ummar Musulmi.
Wannan sulhun bai dauke masa nauyin da Allah ya dora masa na shugabancin Al-ummar Musulmi ba, saboda wanda Allah ta’ala ya zaba, ya kuma sanya shi limani, to mutanen da suka ki binsa ko sauraronsa ne suka yi asara. Saboda sun rasha shiriya ta gaskiya, shiriya ta Allah, a dai dai lokacinda Allah ya samar da ita a cikinsu. Don haka al-ummarce ta yi asara. Shi Imam (a) matsayinsa a wajen Allah yana nan. Kuma nai yi asarar wani abu ba.