182-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi da suka cikin cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
////…Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Alhassan Almujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku. A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda Mu’awiya dan Abusufyan ya maida Ziyad dan Sumayya a matsayin dan’uwansa kuma dan Abusufyan. Wanda manzon Allah (s) ya hana hakan, ya kuma bayyana cewa, da na mai aure ne, kuma mazinaci dutse.
Mu’awiya ya sabawa umrnin manzon Allah (s) sannan ya kuma dawo da dabi’ar jahiliya inda eke hakan. Mun bayyana cewa shuwagabanni cikin sahabban manzon Allah (s) da salihan bayi duk sun yi tir da abinda Mu’awiya yayi na sabawa umurnin manzon Allah (s), duk da cewa hakan bai sa sun dawo kan abinda suka tafi a kai ba.
Har’ila yau mun ji yadda wani sahabi da ake kira Abu Maryam Assaluli ya tashi a cikin masallacin umayyawa a Demash ya tabbatar da yadda Abusufyan mahaifin mu’awiya yayi zina da Sumayya mahaifiyar Ziyad wacce ta kasance sananniyar karuwa a garin Ta’ifa kusa da Makka a lokacin.
Daga cikin wadanda suka bayyana rashin amincewarsu da abinda Mu’awiya da Ziyad dan sumayya suka aikata, akwai Imam Al-Hassan dan Aliyu (a) wanda da farko ya rubutawa Ziyad Wasika ya fada masa cewa manzon Allah (s) ya hana abinda suka yi, kuma yana cewa: da ga mai shimfida (ko aure) sannan mazinaci kuma dutse).
Sannan sun sake haduwa da shi a gaban Marwan dan hakam, da Amru dan Asi da kuma shi Mu’awiya, inda ya fadawa Ziyad, me ya hadaka da kuraishawa? Mu bamu taba sanin sumayya mahaifiyarka ko daya daga cikin kakanninka ya na da nasaba da kuraishawa ba, ya ce masa Sumayya ta isheka kamar yadda manzon Allah (s) ya ishemu.
A nan yana nufin manzon Allah (s) ya ishemu, don su ma ta Fatima diyar manzon Allah (s) mahaifiyarsu ce suka hadu da manzon Allah suka sami wannan daukakar. Don haka ba wajibi ne sai ka nemi dangin mahaifinka ba, ko sai ka samarda da iyaye ta bangaren mahaifinka ba.
Banda shi kaninsa Imam Al-Hussain (a) shi ma ya rubutawa Ziyad ko mu’awiya wasika yana nanata abinda Imam Al-Hassan ya fada.
Banda su hatta Yunus dan Ubaid, wanda ya zo gaban Mu’awiya yana cewa: Ya Mu’awiya manzon Allah(s) yayi yanke hukunci kan cewa da ga mai shimfida (aure) sannan wanda yayi zina kuma dutse, kai ka hukunta da ga mai zina ka sabawa manzon Allah ka sabawa littafin Allah ta’ala ka sabawa sunnar manzon Allah (s) tare da shahadar Abu Maryam wanda ya tabbatar da zinin Abusufyan.? . sai Mu’awiya ya yi barazanar kasheshi,
Sai yace, ba dai zuwa ga Allah ne zan koma ba. Sai Mu’awiya yace: Eee.
Sannan Abdurrahman dan Hakam, dan uwan Marwan dan Hakam, daga cikin Banu Umayya, shi ma bai amince da abinda Mu’awiya yayi ba. A lokacinda ya zo ya fada masa, Mu’awiya ya bawa Marwan dan uwansa umurnin ya fitar da shi daga inda yake.
Sai kuma Abul-Aryan, wanda ya kasance makaho a lokacin, ya yi inkarin abinda Ziyad da Mu’awiya suka yi. Wata rana ya ji hayaniyan mutane sai ya tambaya, yana cewa wani hayaniya nake ji sai aka ce masa|: Ai tawagar Ziyad dan Abusufyan ne! sai yace: Wallahi Abusufyan bai bar wani ba sai Yazid da Mu’awiya da Utbah, da Ambisah da Hanzalah da Muhammad, daga Ina Ziyad kuma ya zo.
Sai labara ya kai kunnan Ziyad, sai ya nemi shawara aka ce masa ya aika masa da kudi, don rufe bakinsa. Saboda mutum ne mai baki. Sai Zayad ya aika masa dinari 200. Da aka kai masa sai yayi farin ciki, ya godewa Ziyad. Sannan wata rana da Ziyad yana wucewa da tawagarsa kamar yadda ya saba. Sai Abul Aryan ya fara ihu yana kuka da aka tambayeshi dalili, sai ya ce: Na tuna da sautin Abusufyan daga sautin Ziyad,
Kunji abinda kudi yake yi, ya sauya gaskiya ta zama karya a lokaci guda, ya kuma sauya imanin mutum daga goyon bayan gaskiya ya zama yana goyon bayan karya da kage. Allah ya kiyayemu.
Sai Abu Bakratah dan uwan Ziyad shi ma dan Sumayya ne, ya yi inkarin abinda dan’uwansa Ziyad da kuma Mu’awiya suka yi. Ya kauracewa masa gaba daya. Sai zuwa wani lokaci wanda Ziyad din zai je aikin hajja, sai Abubakrata ya dauki wani yaronsa ya je gidan Ziyad, wani daga cikin masu gadinsa ya ganshi ya je ya fadawa ziyad, sai ziyar ya jirashi ya karaso wajensa.
A lokacinda ya tsaya a gabansa, sai yayi kamar yana magana da dansa, Ziyad yana ji, yace: Ya dana babanka ya aikata laifi babba a musulunci, mahaifiyarsa ta yi zina, sai ya baranta daga mahaifinsa, kuma na rantse da Allah ban taba sanin Sumayya ta taba ganin Abusufyan ba. Sannan babanka yana son ya aikata laifin da yafi wannan. Yana son zuwa aikin Hajji, kuma zai hadu da ummu Habiba diyar abusufyan daga daga cikin matan manzon Allah (s) (wato ummahatil Muminina), idan ta yi masa izinin shiga wajenta ta aikata babban laifi na karya ga manzon Allah (s) kuma musiba ce, idan kuma ta hana shi shiga wajenta, abin kunya babba ga babanka.
Sai ya juya ya tafi. Sai ya ziyad yace: Na gode maka ya dan’uwa na, kan wannan nasihar, kana fushi da ni ko kana mai yarda da ni.
Sai kuma Yazid dan Mafragh wani mawaki babban da suka yi zamani da ziyada, inda yayi baitoci biyu yana aibata Ziyad da amincewa da zama dan abusufyan bayan shi dan zina ne. Yana ncewa:
Kayi tunani, a cikin tunaninka akwai darasi-Shin ka sami daukaka ne in banta sanyaka shugaba?
Sumayya ta rayu iya rayuwarta bata taba sani ba-Kan cewa danta yana cikin dangin Kuraishawa ne ba a cikin jama’a.
Sai Hassan al-Bisri ko Basri, inda yake cewa: Halaye 4 na Mu’awiya, da daya ne kawai daga cikinsu ya aikata da ya isheshi musiba da sabon Allah babba, kwace shugabancin wannan al-umma tare da amfani da wawayenta, al-hali akwai sauran sahabban manzon Allah salihai a raye, kuma ba tare da shawara ba, sanya dansa (yazid) magajinsa mashayin giya, mai sanya rigunan Al-Harir da dibaji, da maida Ziyad dan Abusufyan alhali manzon Allah (a) yace: Da ga mai aure ko shimfida wanda yayi zina kuma dotse. Sannan bone ya tabbata a gareshi kan kissan Hijir dan Adiy, ya nanata har sau biyu.
Wannan kadan ke nan daga cikin fitattun mutane bayin Allah wadanda suka yi inkarin maida ziyar dan Abusufyan, wanda Mu’awiya yayi a lokacin Khalifancinsa. Sannan ya bashi walin Kufa ya je ya kashe Shi’ar Amirulmumina(a) dama ya sansu. Malaman tarihi sun bayyana cewa a lokacinda Ziyad ya isa Kufa a matsayin Walin Mu’awiya sai ya bukaci wani abu daga wajensa, sai suka ce masa fada, sai ya ce yana son su dangantashi da Abusufyan sai suka ce: Ba zamu yi shaidar Zurba. Don haka tun ba’a je ko ina ba mutane sun ki amincewa da wannan sabon da suka aikata. Amma duk da haka Banu umayya sun sanya sunan Ziyar a matsayin dan Abusufyan a cikin diwanin Quraishawa, wannan halin ya ci gaba har zuwa karshen daular Banu Umayya, sannan har zuwa zamanin sarki Mahdi daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa, sai ya cire sunan Ziyad acikin diwanin Quraishawa. Aka kuma rufe baban ziyar da Abusufyan gaba daya.
Yanzu kuma sai Ma’aikatan Mu’awiya dan Abusufyan, wadanda suka taimaka masa wajen azabtar da al-ummar musulmi da kuma wawason dukiyoyinsu. Mu’awiya dan Abusufyan wanda ya assasa daular Umayyawa. Ya yi amfani da mutane wadanda suka yi fice a kekacewar zuciya wajen mulka da kuma tafiyar da harkokin shugabnanci a kan al-ummar musulmi daga ciki har da zababbun sahabban manzon Allah (s) wadanda ya kashe da dama daga cikinsu a cikin shekaru 20 da yayi yana mulkinsu kafin ya halaka. Amma kuma dan sa Yazid da wadanda suka zo dagabayan sun ci gaba da wannan salon na mulkin da ya kafa har sai da aka kauda su kan kujerar sarautar musulmi a cikin tsakiyar kani na biyu bayan hijira. Ya yi amfani da mutane masu mummunan tarihi a rayuwarsu don cimma manufofinsa daga cikin su, zamu fara da
01-Samrata dan Jundubin, wanda ya kafa tarihi a kekacewar zuciya da zubar da jinin al-ummar Musulmi, ya kuma bakanta tarihin addinin musulunci har duniya ta nade ba za’a taba manta da shi ba. Wannan shakiyyin ya shahara da munafurci hatta a zamanin manzon Allah (s), daga ciki malaman tarihi sun bayyana cewa a zamanin manzon Allah (s) kan cewa Samrata dan Jundubin ya takurawa wani mutumin Ansar kan wata itaciyar dabino da yake da ita kusa da gonarsa, dabonon ta karkatar da yayanta cikin gona ko lambun wannan mutumin ansar, sai Samrata yana shigar lambunsa ba tare da neman izini ba, don ya je wajen itaciyar dabinonsa. Sai ba ansaren ya kai kararsa wajen manzon Allah(s) wanda ya sa aka kira shi.
Sai manzon Allah (s) yace masa: Ka saidawa wannan ba ansaren dabinonka ka karbin kudinka ko ladaka. Sai Samrata yace: Ba zan saida shi ba. Sai yace masa. To ka sayi lambunsa . Sai ya ce b azan saya ba. Sai yace masa. To ka barman itaciyar na yi maka lamuni zaka shiga Aljanna. Sai yace ba zai yi ba.
A lokacinda manzon Allah (s) ya ga taurine kan samrata sai ya juya wajen mutumin Ansar ya ce masa: Ka je ka sare wannan itaciyar dabinon nasa, ka yi jifa da ita, a halin yanzun kuma bai da wani hakki a kanta. Yana fushi ya juya ya barshi.
Wannan ya nuna cewa samrata munafiki ne wanda baya bin umurnin manzon Allah (s), hatta ya kaiga baya son aljannan da manzon Allah (s) yayi masa al-qawali kan itaciyar dabino guda. Ku gaya mani wannan sahabin wanda baya ganin mutuncin manzon Allah (s) me za’a yi da shi. Zamu ga abinda ya aikata bayan manzon Allah (s) wanda ya fi abinda muka fada muni, a cikin shirimmu na gaba.