Kissoshin Rayuwa Fatimah Azzahra(s) 68

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtdha Muttahari ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da kuma.

///… Masau sauraro, idan kuna tare da ya gabata a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon All..(s), kuma mahaifiyar shuwagabannin samarin Aljanna, Alhasan da Alhusain(a), da muke kawo muku. A cikin shirimmu da ya gabata, munji yadda wafatin Zahra(s) ya kasance, da kuma wasiyyar da tayiwa mijinta kuma shugaban muminai Aliyu dan Abitalib (a). Da kuma yadda mutanen Madina suka zo suka cika kofar gidanta (s), don jana’izarta.   Har’ila yau da yadda Asma’u diyar Umais ta hana A’isha matar Manzon All..(s) shiga wajen Zahra(s) bayan wafatinta, sannan Asma’u ta bayyana cewa itace ta yi wasiyar kada a bar wasu mutane su shiga wajenta.

Daga karshen munji yadda Aliyu(a) ya bada umurni, a fadawa mutane, an jinkirta jana’izar diyar manzon All..(s) cikin daren nan. Sai mutane suka waste, suna tsammanin za’a yi shi gobe da safe.

Amma cikin dare, bayan da gari yayi shiru, idanu sun yi barci, sai Aliyu dan Abitalib(a) ya tashi yayi mata wanka, da dukkan abubuwan da yakamat a mamaci. Kama daga wanka, likkafo da Hanud da sauransu.

Mun bayyana cewa ya yi mata likkafi da kellaye 7, a kuma kan kayan da ta yi wafati a cikinsu. Banda haka mun bayyana cewa an yi mata Hanud da Hanud din da aka kawowa manzon All..(s) daga Aljanna.

Mun bayyana cewa ma’sumi ne kawai zai yi wa ma’sumu irinsa. Don haka Aliyu dan Abitalib (a) ne kadai ya cancanci  yayi wa manzon All..(s) wanka, kuma shi ne yayiwa matarsa Fatima (s) diyar manzon All..(s) wanka da sauran abubuwab da akewa mamata masulmi.

A lokacinda ya kammala, sai Imam (a) ya ga marayunta suna kallon jana’izar mahaifiyarsu, mai tausaya masu, a nannade  cikin likkafaninta.

Wannan lokaci ne, wanda ba za’a sake ganin irinta ba, a nan sai mahaifinsu, ya ji tausayinsu, don haka bai, dinke likkafanin  da zare ba, wato suna iya zuwa su ga fuskanta, su kuma yi bankwana da ita. A nan sai ya kirasu da murya, hade da kuka a cikinta, yana cewa: Ya Hassan!! Ya Hussain !! Ya Zainab!! Ya Ummu Kulthum !! ku zo ku yi guzuri daga mahaifiyarku, wannan shi ne rabuwa ta karshe, aljanna ce mahada.

Sai suka taho da sauri, dama sun dade suna jiran wannan damar, don bankwana da mahaifiyarsu, suna kuka suna bayyana bakin cikinsu da rabuwa da Haura’a (s). Sai suna ta jefa kansu a kan gawar mahaifiyarsu mai tsarki, ko wannan yana daga cikinsu yana kuka, ko tana kuka,  suna ta bayyana bakin cikinsa da rabuwa da mahaifiyarsu mai tausayi da kuma jinkai.

Alhassan Da Alhussain suna cewa: kaiton asarata wacce bata yankewa, daga rashin kakammu Muhammad Almustafa (s), da kuma mahaifiyarmu Fatimah Azzahra (s). Ya!! Umman Hassan, kuma ya Umman Hussain, idan kin hadu da kakammu Muhammad Almustafa (s) ki isar da sallamammu a gareshi. Ki fada masa cewa: Mun zama marayu bayanka, a gidan duniya.

Suna zubar da hawaye suna kuma kuka a hankali, Sun yi kuka har  sai da suka jaka wani bangare na likkafaninta(s) da hawayensu.

A nan sai an yi wata karama, wacce ta keta dabi’a, inda, ta fidda hannunta ta rungumesu, daya bayan daya, suna cikin wannan halin, sai Aliyu (a) ya ji murta tana cewa masa ‘dagasu ya Aliyu, hakaki sun sa mala’ikun sama kuka’. Hakika masoya yana shaukin haduwa da juna.

Daga nan kuma, lokacin sallar Jana’iza ta zo da kuma lokacin bisnewa a cikin kasa. Kafin haka an rika an ayyana wadanda zasu zo su halarci sallar da kuma sauran abinda ya rage.

Su ne wadanda basu zalunceta ba, basu kuma kasance masu yin shiru a gaban wadanda suka zalunceta. Sun tsaya tare da ita har zuwa karshe. Basu kasance cikin wadanda suka zauna gefe suna kallonta tana gwagwarmaya da wadanda suka kwace hakkinta ba.

Sune suka fito daga gidajensu a tsakiyar dare, suna tafiya a hankali don kada sauran mutane su sani. Tun lokacinda aka jinkirta yi mata jana’izar sai aka fada masu lokacin da za’a yi mata (s) sallar. Don haka an gudanar da sallar jana’izar cikin nutsuwa da rashin hayaniya. Imam Ali (a) ya dauki wannan matakin ne, don tabbatar da cewa ya aiwatar da wasiyarta (s).

Sun sami damar halattar Jana’izar, kuma sune: Salman Alfarisi, da Ammar dan Yasir da Abuzarl Ghifari, Miqdad dan Aswad da Khuzaifatul Yamani, Abdullahi dan masa’ud, Da Abbas dan Abdulmuttalib, da Fadlu dan Abbas, Da Akilu dan Abitalib, da Zubair dan Awwam, da Buraidatul Aslami, da wasu mutane daga banu Hashim.

Sune suka yi sallah suka kuma yi rakiyar Jana’izarta(s) zuwa masaukinta na karshe cikin dare. Haka a ka yi Jana’zar Fatimah Azzahra (s), diyar manzon All..(s) tilo wacce ya bari a bayansa, amma an mata jana’iza kamar bakuwa wacce bata da kowa a gari.

An yi mata Jana’iza kamar ba ta da matsayin da take da shi a wajen All..T.  Wadannan sune suka rabauta da sallah da kuma rakiyar gawar Fatimah (s) shugaban mata a gidaje biyu, wato duniya da Aljanna.

Imam Ali (s) ne ya jagoranci sallar sannan Alhassan da Alhussain suna bayansa(s), yana fada a cikin addu’arsa.

“Ya Ubangiji !! na yarda da diyar annabinka (s), Ya Ubangiji !! Hakika an sanyata kewa, ka debe mata kawa, Ya Ubangiji an kaurace mata, ka sadar da ita, Ya Ubangiji !! Hakiki an zalunceta, ka yi hukunci kan hakkinta, Lalle kaine, mafificin masu hukunci.

Da ya kammala salar Gawarta mai tsarki, sai ya yi sallah raka’o’ii biyu, sannan ya daga hannayensa sama yana cewa: Wannan itace diyar annabinka Fatimah(s), ka fitar da ita daga duffai zuwa haske. Sai ka sa ta yi haske….

Sannan Amirulmuminina (s) ne, ya yi mata sallah, saboda ita ma’asuma ce, dole ne sai masumi ne zai yi mata sallah. Kuma sallah ga mamace addu’ace gareshi, don samun rahamar All..T. Amma ga ma’asumai addu’a a kan gawarsu, yana daga cikin wajibin sauran ma’asumai ne. Wannan a bangaren shari’a kenan.

Amma a hankalce da kuma hikima, Fatimah (s) duk tare da matsayinda All..T ya bada, da daukakan da take da shi, ta je har gaban shugaban daula na lokacin tana neman hakkinta, ba’a bata ba, sannan ta yi khuduba a cikin masallacin mahaifinta manzon All..(s) ba wanda ya tanka mata. Banda haka, mijinta Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) ya dauketa sun yi ta yawo cikin madina gida-gida suna neman taimakon sahabban manzon All..(s) daga muhajirun da Ansar, suna neman taimakonsu  don a maida masu hakkinsu, amma bata samu masu taimakonta ba.

Sannan an ji mata ciwo a jikinta a ranar da aka fitar da mijinta da karfi, daga gidanta don yayi bai’a amma ya ki hakan. Sun wulakantata, matuka, duk tare da matsayinta a duniya da Lahiri.

Ayoyin Al-kur’ani sun sauko da hakkinta, amma aka hanata, sanna anki a yarda da hatta shaidunta wadanda suke tabbatar da hakkinta. Don haka tana da hakki, ta dauki  mataki a kan irin wadanan mutane.

Don haka ne ta yi wasiya kan cewa kada wani, wanda ya cutar da ita ko ya ya yi banza da ita ya halarci jana’izarta, kuma kada ma,  su san inda kabarinta yake.

Wannan don ya zama shaida a gareta ga al-ummar mahaifinta wadanda za su zo daga baya, kan cewa, an zalunceta kuma zaluntan da aka yi mata, zai wanzu har zuwa ranar kiyama.

Kamar yadda muka karanta a baya, Zahra (s) ta bar wasiyya kan kada a bayyana kabarinta, a boye shi, saboda sakon zaluntarta ya kai ranar kiyama. Musamman ga mahajjata, wadanda suke ziyartar manzon All..(s) da sauran shuwagabanni a Madina, zasu nemi kabarinta ba zasu gani ba, sai su tambaya, me ya faru da ita ? ina ne kabarinta ? ba za su ganeta ba har tashin kiyama.

Don haka a tsawon tarihin musulunci, malamai sun yi ta sabani a kan inda kabarinta(s)  yake, wasu sun ce an bisneta ne a makabartan Bakiyya, wasu kuma suke ce an bisneta a cikin dakinta. Don haka a lokacin da aka fadada masallacin manzon All..(s) kabarinta ya dawo cikin masallacin.

An ruwaito cewa Imam Ali (s) ya tuna kaburbura da dama a makabartan bakiyya, don batar da mutane ne, don kada, su san inda kabarinta yake. Kuma ko da a baki’a ne, ya yi mata kabari,  ba wanda ya san kabarinta har yanzun shekaru kimani 1,400 da wafatinta.

Ko a ina aka yi mata kabari dai, abinda ya faru shi ne, an tona mata kabarin Lahdu, a wani wuri, inda mutane 4 suka rike gawarta mai tsarki kuma marasa nauyi, saboda ramewanta(s). Kuma sune Aliyu dan Abitalib(a) da Abbas dan Abdulmuttalib, da fadlu dan Abbas da wani mutum na 4.

Sannan Aliyu dan Abitalib (a) a matsayinsa na mai kula da al-amuranta ya shiga cikin kabarin ya kuma karbota, ya sata a cikin lahadunta. Yana mai cewa: “Ya ke kasa, na baki ajiyar, abin ajiya ta, wannan itace diyar manzon All..(s).

An karbo hadisi daga Imam Sadik(a) yana cewa: A lokacinda Aliyu (a) ya Sanya Fatimah (s) a kabarinta yace: Da sunan All..mai rahama mai jinkai, da sunan All..da kuma All..a kuma kan tafarkin mazon All..muhammad manzon All..(s). Na mika ki, Ya ke Siddika ga wanda ya fi cancanta da ke banda ni. Kuma na yerje maki abinda All..ya yerje maki.

Sannan ya karanta aya wacce take cewa: {Daga gareta muka halicceku, kuma a cikinta zamu maida ku, kuma daga gareta ne zamu fitar da ku a wani karon.}

To masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullhi wa barakatuhu.

===================================================.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments