Shugaban majalisar dokokin kasar iran mohammad Baqeer Qalibaf ya bayyana cewa kasar iran ba za ta bari jinann shaidai da aka zubar musamman na jagoran juyin musulunci na kasar Ayatullah sayyid Ali Khamena’i da suka yi shahada sakamakon harin da Amurka da Isra’ila suka kai ya tafi a haka nan ba,
Shugaban majalisar yayi wannan bayani ne a lokacin da ake bikin tunawa da yara yan makaranta na garin minab guda 168 da suka yi shahada sakamakon hari da Amurka da Isra’ila suka kai musu a ranar 28 ga watan fabarerun shekara ta 2026 da muke ciki,
Haka zalika ya sha alwashin cewa bisa jagorancin jagoran juyin musulunci na yanzu Ayatollah sayyid Mujtaba Khamina’I iran za ta sadaukar da dukkan karfinta wajen kare hakkokin alummar kasar, da kawo karshen yan mamaya, da kuma ladabtar da azzalumai da kuma daukaka matsayi da martabar kasar A gefe guda kuma shugaban majalisar yace Iran ba zata taba bude mashigar Hurmuz ba wadda aka rufe don mayar da martani kan hare haren yan kasashen waje, kuma dole sai Amurka ta cire killacewar taku da ta yi wa kasar iran . kuma iran ta yi gargadin cewa Asheriya take ta sake turmusa hancin makiya idan suka sake kai mata hari.