Rahotanni sun bayyana cewa kwamandan dakarun kare juyin musulunci na iran Major Ganeral Ahman Vahidi ya bayyana cewa dole ne kasar iran ta ci gaba da karfafa bangaren tsaronta da kuma karfin mayar da martani domin makiya ba za su taba zubar da makaman yakinsu kan alummar Iran ba.
Kwamandan yayi ishara game da irin dabarun da zaa yi amfani da su game da ci gaba da ake samu a yankin, musamman bayan hare-haren baya bayan nan na Amurka da isra’ila suka kaddamar kan kasar iran babbar hujja ce da take kara tabbatar da cewa makiya ba za su dena nuna kiyayya da kulla makirci a kan kasar iran ba
Da yake Magana game da kiyayyar da amurka da isra’ila suke nuna wa iran yace iran za ta ci gaba da kera makaman kariya da kayyayakin aiki na Soji da dukkan karfinta cikin sauri da kuma amfani da hikima.
Daga karshe kwamandan ya kammala sakonsa da mika ta’aziya ga shahidan da suka kwanta dama wajen kare kasar, kuma ya jinjina game da yadda aka ci gaba da bin abin da suka bari na kishin kare kasa.