Iran Tace Tana Kokarin Ganin Ta Cika Alkawulan Da Ta Daukawa Bankin Raya Kasashen Musulmi (IDB)

Ministan tattalin arziki na kasar Iran ya gana da shugaban bankin raya kasashen musulmi wato ‘Islamic Development Bank’ a birnin Riyad na kasar Saudiya. Ya

Ministan tattalin arziki na kasar Iran ya gana da shugaban bankin raya kasashen musulmi wato ‘Islamic Development Bank’ a birnin Riyad na kasar Saudiya. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin JMI tana iya kokarinta don cika alkawulan da ta daukarwa bankin.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Nasir Himmati ministan tattalin arziki na kasar  Iran yana fadar haka a lokacin ganawarsa da shugaban bankin Sulaiman Jabir a taron bakin karo na 28 a birnin Riyad na kasar Saudiya a jiya Litinin.

Nasir Himmati ya kara da cewa, gwamnatin JMI tana fatan bankin raya kasashen musulmin, zai tallafawa wusu manya-manyan ayyuka a jumhuriyar musulunci ta Iran.

Sulaiman Jabir a nashi bangaren ya bayyana cewa JMI tana daga cikin kasashe masu jari mai yawa a bankin, sai dai , takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa JMI suna hana bankin aiki yadda yakamata da JMI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments