Hukumar bunkasa harkokin kasuwanci na kasar Iran ta bada sanarwan cewa kasar Qatar ta sake bude tashar jiragen ruwa na kasar Al-Ruwais ga jiragen kasuwanci na kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran, ya nakalto Abbas Abdolkhani shugaban hukumar yana fadar haka ya kuma kara da cewa kafin haka jiragen ruwa dauke da kayakin kasuwanci na kasar Iran daga tashar jiragen ta Dayyer na zuwa Al-Ruwais inda ya ke isar da kayakin Iran zuwa kasuwannin kasar.
Abdolkhani ya bayyana cewa, wannan matakin yana da kyau, kuma zai kara dakon zumunci tsakanin kasashen biyu. Kuma a halin yanzu ana tattaunawa, don kara yawan kayakin Iran da ke shiga kasar Qatar.
Abdolkhani ya bayyana cewa jakadan kasar Iran a birnin Doha ne ya kai kawo don tabbatar da harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya sake dawowa.