Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran isma’il Baqai yayi tir da sanarwa da Amurka ta fitar na kakaba mata sabon takunkumi , yace matakin ya wuce batun matsin tattalin arziki akan Tehran yunkuri ne na keta yanci da hakkokinta.
A cikin wani bayani da wallafa a shafinsa na X kakakin yace kasar Amurka ta sanar da kakaba sabon takunkumi kan kasar iran , wanda wannan ya wuce batun takunkumin karya tattalin arziki kan wata kasa, cin zarafi ne da kuma keta yancin kasar mai cin gashin kanta kuma mamba a majalisar dinkin duniya.
Wannan bayani ya zo ne bayan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya fitar na sanya wa Tehran sabon takunkumin karyar tattalin arziki a ranar larba da ta gabata, tare kuma da yin barazana ga duk wata kasa da ta ci gaba da huldar tattalin arziki da Tehran to za ta fuskanci mataki mai tsanani
Har wa yau ya kara da cewa duk wata kasa da ta bada dama ga Tehran wajen gudanar da huldar kasuwanci ko zirga zirgan jiragen sama ko kuma wata gwamnati ta bada wata gudunmawa da ta shafi gudanar da rayuwa ga iran to zata fuskanci mummuna takunkumin karyar tattalin Arziki.
Ana sa bangaren ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi da yake mayar da martani kan sabon takunkumin yace wannan sanarwar ta trump tamkar sauran takunkumin karya tattalin arziki ne da Amurka ta sanyawa Tehran na tsawo shekaru 14 da suka gabata da bai yi nasara ba, don haka shi ma wannan ba zai yi nasara ba.