Iran Ta Yi Tir Da Birtaniya Kan Ayyana IRGC a Matsayin Barazana

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na ayyana Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na ayyana Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “barazana a karkashin Dokar Tsaron Kasa ta Burtaniya,” tana mai kiran matakin “mara adalci da rashin da’a” wanda kuma ya saba wa dokokin kasa da kasa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta ce matakin ya saba wa “ka’idoji da dokokin kasa da kasa, da rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na wasu kasashe.”

A cewar sanarwar, IRGC muhimmin bangare ne na rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma tare da sojojin Iran, suna da alhakin kare mutuncin yankunan kasar, hurumi, da tsaron kasa.

Ma’aikatar ta kuma kare rawar da IRGC ke takawa a yankin, tana mai cewa gudummawar da take bayarwa ga zaman lafiya, tsaro, da mutuncin dan adam a yankin, musamman ta hanyar yakar kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh, an amince da ita a duk duniya.

A cewar sanarwar, shawarar da Birtaniya ta yanke na sanya wa wata hukuma ta kasa mai ‘yancin kai irin wannan suna, wani abun kunya ne.

Ma’aikatar ta kara da cewa wannan matakin bai dace ba musamman idan aka yi la’akari da rikicin da ke faruwa a Yammacin Asiya.

Iran ta musanta zarge-zargen Birtaniya kan IRGC, tana mai kare hakkinta, na daukar matakin ramuwar gayya akan wannan matakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted