Rundinar Kare Juyin Juya Halin Musulinci Ta Iran, ta sake gargadi ga makiya akan duk wani yunkuri na sake kai wa kasar hari.
Babban kwamandan rundunar ta IRGC, Manjo Janar Ahmad Vahidi, ya bayyana cewa abinda makiya suka gani zuwa yanzu mafari ne kawai, yana mai gargadi game da ci gaba da kai wa kasar hari.
A lokacin ziyarar da aka kai a ranar Asabar, a wani sabon sansani na ” makamai masu linzami na IRGC,” Janar Vahidi ya jaddada cewa kasashen da ke cikin NATO sun hada kai kan Iran ba tare da cimma burinsu ba.
Wannan yana nuni ne ga goyon bayan da wadannan kasashe suka baiwa hadin gwiwar Isra’ila da Amurka.
Janar Mousavi ya kara da cewa an karfafa karfin Rundunar Sojan Sama ta IRGC a tsakanin yake-yake biyu da Amurka da Isra’ila suka shelanta kan Iran.
Ya jaddada cewa Rundunar Sojan Sama ta IRGC ta kirkiro tsare-tsare da kayan aiki masu inganci na musamman wadanda aka tsara don hana kowace barazana.
Ya yi ikirarin cewa rundunar sojin sama ta IRGC ba za ta yi jinkirin daukar fansa kan duk wani hari ba.
IRGC ta bayyana wani sabon makami mai linzami wanda zai iya, a karon farko, daukar makamai masu linzami guda biyu a lokaci guda.