Iran Ta Gabatar Da Kara Dangane Da Kissan Jagora(q)

Mai gabatar da kara a nan Tehran ya bayyana cewa an gama bincike kan kissan Jagoran juyin juya halin musulunci da iyalan gidan sa, da

Mai gabatar da Kara

Mai gabatar da kara a nan Tehran ya bayyana cewa an gama bincike kan kissan Jagoran juyin juya halin musulunci da iyalan gidan sa, da kuma yan makarantar Minab wadanda Amurka suka yi a farkon wannan Shekara.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ali Salehi yana fadar haka, ya ce sun kuma fayyace wadanda suke da hannu a cikin kissan.  Kuma a halin yanzu an tabbatar da wadanda ake tuhuma.

Ya ce ‘kai hare hare kan mai mukami mafi girma a kasar suna nufin wargaza kasar”. Yace laifukan da suka yi ya dace a hukuntasu a bisa dokokin cikin kasa da kuma na kasa da kasa.

Ya ce wadanda aka kashe a wadannan hare hare ba za’a dauke su a matsayin ‘cutar da wanda ba’a yi nufin cutar da su ba’.

Yace mata da yara da wadanda ba ruwansu da yakin da aka ce, ana iya sanyasu karkashin ayyukan ta’addancin da wadannan masu zubar da jinni suka yi a farkon yakin da suka dorawa a Iran a farkon wannan shekara.

Ali Salehi yace a bincike da shaidun da suka tare ya kai matsayin a gabatar da su a kotuna na cikin gida haka ma a kotunan kasa da kasa, don bin hakkin wadanda aka aikata ayyukan ta’addanci a kansu. Ya kuma kawo sharuddan da aka da su a fagen kasa da kasa don tammabar da zargi ko laifi a kan wadan da suka aikata laifi.

Yace a halin yanzu dai, bayan kammala aiki sun gabatar da karar a gaban kotu ana kuma jiran hukunci na kashe daga bakin alkali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted