Iran Ta Ce: Ba Zata Taba Amincewa Amurka Ta Shiga Cikin Masu Kula Da Mashigar Ruwan Hormuz Ba

Hedikwatar Khatam al-Anbiya ta jaddada cewa: Ba zasu bari Amurka ta tsoma baki a harkokin tafiyar da mashigar ruwa ta Hormuz ba Hedikwatar rundunar sojin

Hedikwatar Khatam al-Anbiya ta jaddada cewa: Ba zasu bari Amurka ta tsoma baki a harkokin tafiyar da mashigar ruwa ta Hormuz ba

Hedikwatar rundunar sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta yi gargadi game da duk wani tsoma bakin Amurka a harkokin gudanar da mashigar ruwan Hormuz, tana mai jaddada cewa: Iran ba za ta taba barin Amurka ta yi hakan ba. Ta kuma yi gargadi ga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya game da yin hadin gwiwa da sojojin Amurka, tana mai cewa irin wannan hadin gwiwa za a dauke shi a matsayin wani mataki na cin zarafi ga ikon mallakar Iran da tsaron kasarta.

Kakakin hedikwatar Tsakiyar ta rundunar sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta Iran ya tabbatar da cewa: Iran ba za ta bar Amurka ta tsoma baki a harkokin gudanar da mashigar ruwan Hormuz ba, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa na kasashen yanki da Amurka ko kuma samar da tallafin dabaru ga sojojinta ya zama wani mataki na cin zarafi ga ikon mallakar Iran da tsaron kasarta.

A cikin wata sanarwa, kakakin ya ce: Ci gaba da kasada da kuma ayyukan nuna kiyayya da Amurka ke yi na tsoma baki a harkokin gudanar da mashigar Hormuz na barazana ga tsaron yanki, cinikayyar kasa da kasa, da kuma motsin jiragen ruwa na mai da jiragen ruwa na kasuwanci. Ya tabbatar da cewa hadin gwiwar wasu kasashen yankin da Amurka na kara hadarin barkewar yaki mai fadi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted