HKI Ta Kai Wa Karamin Ofishin Jakadancin Iran A Kasar Syria Hari

 Kafafen watsa labarun Syrai sun ambaci cewa da marecen jiya Litinin jiragen yakin HKI sun kai hari akan karamin ofishin jakadancin Iran dake birnin Damascuss.

 Kafafen watsa labarun Syrai sun ambaci cewa da marecen jiya Litinin jiragen yakin HKI sun kai hari akan karamin ofishin jakadancin Iran dake birnin Damascuss.

A sanadiyyar harin dai dukkanin ginin karamin ofishin jakadancin na Iran ya zube kasa, tare da yin shahadar wasu ma’aikata da kuma jikkatar wasu.

jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a Syria Hussain Akbari ya bayyana cewa; Sojojin HKI sun kai harin ne akan ginin mai hawa shida, kuma a lokacin harin ina ofis wajen aiki.

Shi kuwa ministan harkokin wajen kasar Syria, Faysal Mikdad wanda ya ziyarci ofishin jakadancin Jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi Allawadai da harin na  HKI, yana mai kara da cewa; Babu yadda za a yi ‘yan sahayoniya su iya cutar da alakar dake tsakanin Syria da Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments