A wani bayani da ‘yan majalisar dokokin kasar Lebanon masu wakiltar Hizbullah da aka fi sani da ” Wafa’u-Lil Muqawamah” ta bayyana cewa; Tarukan Arba’in na Shahadar Imam Hussain ( a.s) da aka kallama suna a matsayin wani ginshikin fada da zalunci wuce gona da iri, don haka yin fada da zalunci wani nauyi ne ta fuskar halayyar kwarai.
Haka nan kuma bayanin ya yi watsi da duk wata barazana da tsoratarwa da zummar tilasta al’umma ta mika kai.
Bayanin ya yi suka akan siyasar Amurka a cikin wannan yanki tare da kare hakkokin al’ummu na zabar salon siyasar da suke so,nesa matsin lamba da tsokana.
Dangane da tattaunawar da gwamnatin Lebanon take yi da yan Sahayoniya, bayanin ya yi kira da a dakatar da shi domin babu abinda ya jawo wa al’ummar kasar sai asara
Haka nan kuma bayanin ya yi tir da yadda Haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da kai hare-hare a cikin yankin Gaza da yammacin kogin Jordan.Bugu da kari bayanin ya yi Ishara da tsayin dakar al’ummar Palasdinu da riko da kasarsu da hakurin da suke yi, wanda dalili ne akan cewa za su yi nasara komai dadewar lokaci.