Gharibabadi : Killace Tashohin Ruwa Na Iran, Shelanta Yaki Ne

Wadannan kalamai sun zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa Iran na shinrin keta takunkumin ruwan na Amurka.

Iran ta bayyana killace tashohin jiragen ruwanta da Amurka ke cigaba da yi a matsayin shelanta yaki, tana mai shan alwashin daukar dukkan matakan da suka wajaba don kawo karshen hakan.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ne Kazem Gharibabadi, ya bayyana hakan, tare da bayyana matakin na Amurka da haramtacce.

Mista Gharibabadi ya ce tuni Iran ta sanar da Washington ta hanyar masu shiga tsakani.

Wadannan kalamai sun zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa Iran na shirin keta takunkumin ruwan na Amurka ta hanyar aika ayarin jiragen ruwa na mai zuwa China.

Kuma Tehran, ta ce a shirye ta ke ta kai hari kan wuraren hakar mai na kasashen dake kawance da Amurka idan Washington ta kuskura kai hari kan jiragen ruwan na ta.

Duk da haka, Mr. Gharibabadi ya ce Tehran na fifita hanyar diflomasiyya don warware sabanin da ke tsakaninta da Washington ta hanyar tattaunawa.

Jami’in diflomasiyyar na Iran ya kara da cewa tattaunawa, ta hanyar masu shiga tsakani, ciki har da Qatar, ta ci gaba ba tare da katsewa ba a cikin ‘yan makonnin nan.

 Ya kara da cewa wata tawagar Qatar ta ziyarci Tehran kwanan nan  don tattaunawa da jami’an Iran.

Mr. Gharibabadi ya tabbatar da cewa Iran za ta iya sake bude mashigar Hormuz, muddin Washington ta janye shingen ta kuma saki kaddarorin Iran, saidai Iran ba za ta taba amincewa ta mika tarin uranium dinta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted