Majiyoyin dakarun izzuddin Kassam da kuma Saraya Kudus a Gaza sun bayyana cewa mayakansu sun cilla makamai masu linzami wadanda suke cin karamin zango kan sansanin sojojin HKI a kusa da Asbitin Ashifa a yammacin Gaza, inda suka tarwatsa shi.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyan Saraya Kusdus ta kungiyar Jihadul Islami na bayyana cewa sun sami nasarar halaka sojan yahudawan sahyoniyya guda a gabacin birnin Gaza.
A wani labarin kuma jiragen yakin HKI sun yi ruwan wuta a sansanin yan gudun hijira da ke bakin ruwa a kusa da birnin Gaza inda Falasdinawa 2 suka yi shahada sannan wasu 10 suka ji rauni.