Search
Close this search box.

Gaza: Falasdinawa Fiye Da 70 Suka Yi Shahadi A Gaza A Cikimn Sa’o’i 24 Da Suka Gabata

Sojojin HKI a Gaza suna ci gaba da kissan kiyashin Falasdinawa a yankin, kuma a tsakanin jiya da yau sun kashe Falasdina wa 71 a

Sojojin HKI a Gaza suna ci gaba da kissan kiyashin Falasdinawa a yankin, kuma a tsakanin jiya da yau sun kashe Falasdina wa 71 a yayinda wasu 102 suka ji rauni.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ta nakalto ma’aikatar kiwon lafiya na zirin Gaza na bada wannan sanarwan ya zuwa yanku daga lokacin da aka fara yakin falasdinawa kimani dubu 8 ne suka bace, kuma mafi yawan zaton shi ne suka karkashin burabuzan gine ginen da sojojin HKI suka rusa a kansu.

Rahoton ya kara da cewa a jiya Talata kadai sojojin yahudawan sun kama falasdinawa akalla 40 a yanklin yamma da kogin Jordan, da dama daga cikinsu yara ne.  Sannan a zirin Gaza kadai yan makaranta 6,050 ne suka yi shahada sannan sun rusa makarantu 408.

Banda haka jimmillar mutanen da suka yi shahada, a gaza kadai sun kai 32,916 a yayinda wasu 75,494 suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments