Gaza: Adadin Falastinawa Da Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra’ila Ya Kai 36,171

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar a yau cewa sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra’ila sun aikata kisan kiyashi sau shida kan iyalan Falasdinawa a

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar a yau cewa sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra’ila sun aikata kisan kiyashi sau shida kan iyalan Falasdinawa a Gaza cikin sa’o’i 24, inda suka kashe Falasdinawa 75 tare da jikkata wasu 284 na daban.

Yawancin wadanda abin ya shafa na ci gaba da zama a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, yayin da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke hana motocin daukar marasa lafiya da jami’an agajin gaggawa isa wuraren domin taimaka musu.

Ma’aikatar ta kara da cewa, wannan yasa adadin Falasdinawa da sojojin mamaya na Isra’ila suka  kashe tun daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yau, ya kai 36,171 sannan wadanda suka jikkata adadinsu ya kai zuwa 81,420.

An yi imanin cewa wadannan alkaluma ba su kai yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren Israila a Gaza ba, yayin da hukumomin kiwon lafiya na Falasdinu ke fuskantar kalubale wajen kididdige adadin shahidan da kuma  suka jikkata, kasantuwar akwai dubban mutane a karkashin buraguzan gine-gine da Isra’ila ta rusa gidajensu suna ciki, wadanda ba san iyakarsu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments