An Ji Karar Harbe-Harbe A Barikin Sojojin Kusa Da Tashar Jiragen Sama Na Yemai
Mazauna birnin Yemai babban birnin Jumhuriyar Nijer sun bada labarin jin karar harbe harbe a wani barikin sojoji a daren yau Asabar, bariki wanda aka kai masa hare hare har sau biyu a cikin wannan shekarar da muke ciki.
Shafin yanar gizo na labarai ya bayyana cewa Niger tana fama da yan jihadi daban daban tun fiye da shekaru 10 a kasar Amma bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a cikin watan Yulin shekara ta 2023 yan bindiga wadanda ake ganin yan ta’adda ne dasuke samun goyon bayan kasashen waje sun kai hare hare har sau biyu a cikin wannan shekarar a kan barikin sojoji mai lamba 101 da ke birnin Yemai babban birnin kasar.
Har’ila yau wasu kafafen yada labarai da sada zumunta sun tabbatar da labarin, sun kuma bayyana cewa an kwana ana jin karar tashin bama bamai a kusa da barikin sojojin.
A farmakin da suka kawo cikin watan Jeneru dai an kashe yan ta’adda 20, a barikin, sannan sojoji 4 suka ji rauni a lokacin.
Genar Abdourahamane Tiani, a lokacin ya ce yan ta’addan masu samun goyon bayan kasashen waje suna son ganin bayan dukkan makaman kasar da suka danganci tsaron sama na kasar. Sannan a cikin watan Yuni an kashe sojoji da fararen hula 11 wasu 2 suka ji rauni. Yan ta’addan suna aiki a duk kasashen sahel