Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa Amurka sun nunawa Trump ba sa son yaki a zaben rabin wa’adin da suka gudanar a jiya Talata.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a safiyar yau Laraba a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, hankali da kuma tsadar rayuwa sun sa Amurka suka ce ba mu yard aba, bamu yarda da yaki wanda zai jawo mana tsadar rayuwa ba.
A jiya talata ne aka gudanar da zaben tsakiyar wa’adi wanda jam’iyyar Democrats ta lashe majalisun dokokin kasar Amurka guda biyu, wato sanats da Represantative. Wanda ya zama musiba ga Jam’iyyar Republicans ta shugaba Trump.
Masu nazarin harkokin siyasa, sun bayyana cewa, yawan fitowar zaben ya zama tarihi, don kawo karshen tsadar kayaki.